1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump na fuskantar barazana daga jam'iyyar adawa

Ramatu Garba Baba
September 24, 2019

Bincike ya gano yadda Shugaba Donald Trump ya janye tallafin da Amirka ke bai wa Ukraine a matsayin wani yunkurin jan ra'ayin shugaban kasar don ba shi bayanan sirri kan abokin hamayyarsa.

https://p.dw.com/p/3Q8Gq
Washington Oval Office Donald Trump Telephon
An zargi Shugaba Trump da laifin tursasa shugaban Ukraine ta wayaHoto: picture-alliance/AP/A. Brandon

A yayin da Shugaban Amirka Donald Trump ke fuskantar barazanar neman a tsige shi daga mukaminsa kan wani wayan tarho da yayi da Shugaban kasar Ukraine Voldymyr Zelenskiy, wani bincike ya nunar cewa, Shugaban ya soma yi wa Ukraine din barazana, bayan da ya bayar da umarnin dakatar da tallafin kusan dala miliyan dari hudu da Amirkan ke bai wa kasar, 'yan kwanaki kafin ya nemi jan ra'ayin shugaban na neman ya kaddamar da bincike a game da Joe Biden, babban dan takara na jam'iyyar adawa ta Demokrat.

Shugabanin biyu dai sun yi wayan ne a watan Yunin bana, inda aka danganta yunkurin da neman samun galaba kan Mista Biden da ke zama babban abokin hamayyarsa a zaben da ya ke son sake samun nasarar ci gaba da mulki. Jam'iyyar ta Demokrat, ta zargi Trump da laifin tursasa shugaban wata kasa kan ba shi bayannan sirri,  wanda laifi ne da ya sabawa dokokin kasar ta Amirka.