1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yi watsi da bukatar Iran na yin musayar Fursunoni

Binta Aliyu Zurmi
September 26, 2019

Amirka ta ki amincewa da bukatar musayar Fursunoni da Iran, Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ne ya sheda hakan.

https://p.dw.com/p/3QJLh
Kwafi mahada
Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Mike Pompeo ya ce bai ga yiyuwar yin hakan ba a halin da ake ciki yanzu.

Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaban kasar ta Iran Hassan Rouhani, ke cewa ta hanyar diplomasiya kadai, za a iya magance matsalar rikicin yanki. Rouhani ya ma nemi Amirkan,  da ta fito da sheda kan zargin da ta ke wa Iran, na laifin kai hari a kan rijiyoyin man kasar Saudiya. 

Duk da cewa ya ce a shirye su ke dasu hau teburin tataunawa idan har Amirkan ta janye takunkumin da ta azawa kasar, ana fatan sulhu inda batun musayar fursunonin ke daya daga cikin matakan maslahan.