1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta yi alkawarin sake gina Gaza

Abdullahi Tanko Bala
May 22, 2021

Al'ummar Gaza sun fara kokarin komawa harkokin rayuwa yadda aka saba bayan mummunan barna da aka shafe kwanki goma sha daya ana yi a fadan da Falasdinawan suka yi da Israila da ya hallaka mutane fiye da 200

https://p.dw.com/p/3tow4
Palästina | Zerstörtes Gebäude in Gaza
Hoto: Suhaib Salem/REUTERS

Dubban Jama'a ne dai suka rasa muhallansu a kazamin fadan da aka shae kwanaki goma sha daya ana yi tsakanin Hamas da Israila.

Hukumomi sun raba tantuna da katifu ga mabukata a yankin zirin Gaza bayan tsagaita wuta a tsakanin bangarorin biyu.

A yanzu hankula sun koma ga sake gina yankin wanda ke karkashin ikon kungiyar Hamas. 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 6,000 basu da mastuguni. A waje guda kuma masu aikin ceto na cigaba da laluben baraguzai domin gano gawarwaki ko kuma wani da za a samu da sauran numfashi.

Shugaban Amirka Joe biden ya yi alkawarin taimakawa domin sake gina yankin na Gaza.