1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Larabawa ba sa taimaka wa Falasdinawa inji Amirka

Abdullahi Tanko Bala
July 24, 2018

Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Harley ta ce babu kasashen da suka fi dacewa su taimakawa Falasdinawa kamar makwabtansu na larabawa da kuma saura kasashe na kungiyar musulmi ta duniya OIC amma ba sa yi.

https://p.dw.com/p/321sy
USA Nikki Haley,UN-Sicherheitsrat zu Syrien
Nikkiy Haley Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Hoto: picture-alliance/dpa/AA/A. Ozdil

Jakadar Amirka a majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta soki kasashen Larabawa da sauran kasashen musulmi da yawan babatu akan nuna goyon bayan Falasdinawa amma kuma basa bada gudunmawar kudi domin tallafa musu inda ta ambaci kasashe kamar Masar da Kuwait da kasar hadaddiyar daular larabawa.

Harley ta kuma nuna yadda kasashe irinsu Algeria da Tunisia da Pakista da Oman da kuma Turkiyya walau dai basu bayar da komai ba ko kuma abin da suka bayar din bai taka kara ya karya ba wajen taimaka wa hukumar taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniyar da ke agazawa Falasdinawa 'yan gudun hijira. 

Amirka wadda ita ce ta fi bada tallafin jin kai ga hukumar jin kai ta rage dala miliyan 60 daga cikin alkawarin da ta yi na dala miliyan 365 a bana.