1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Takunkumi kan jagoran Wagner a Mali

May 26, 2023

Ma'aikatar baitil malin Amirka ta sanya takunkumi kan wani dan Rasha da ta ke zargi da jagorantar kamfanin sojojin hayan Rasha na Wagner a Mali.

https://p.dw.com/p/4RpvJ
Sojojin hayan Rasha na Wagner a Mali
Hoto: French Army/AP/picture alliance

Amirka ta ce jagoran,  Ivan Maslov babban jigo ne a harkokin kamfanin Wagner a duniya. Amirkar dai ta zargin kamfanin Wagner da ke aiki a Mali da wasu kasashen Afirka da yunkurin tattara makamai da jirage marasa matuka da kayayyakin yaki domin ci gaba da yakar Ukraine.

Sai dai har kawo yanzu gwamnatin Malin bata mayar da martani kan wannan zargin ba. A share guda Amirka ta zargi kamfanin da bai wa dakarun RSF a Sudan na'urorin kakkabo makamai masu linzami da ta ce ka iya kara musu karfin iko wajen yakar dakarun sojin Sudan.

Kasashen Yamamcin Turai dai na nuna damuwarsu kan ayyukan kamfanin Wagner a Mali tun a shekarar 2021, inda kamfanin ke taimakawa Mali a yakin da gwamnati ke da 'yan ta'adda.