1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta nuna fargaba kan rikicin Burundi

Mouhamadou Awal BalarabeMay 1, 2015

Amirka ta yi barazanar ladabtar da duk wanda za a samu da hannu wajen rura wutar rikicin siyasa da Burundi ke famda shi, sakamakon yunkurin Nkurunziza na yin tazarce.

https://p.dw.com/p/1FIjt
Burundi Proteste
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Kasar Amirka ta nuna fargaba dangane da halin da fagen siyasar Burundi ya samu kansa a ciki, bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya sha alwashin yin tazarce ta ko halin kaka. Manzon da fadar mulki ta Washington ta tura wannan kasa Tom Malinowski ya bayyana cewar Burundi na cikin hadarin sake fadawa cikin yakin basasa.

Jam'iyyun adawa da kuma Kungiyoyyin fararen hula na Burundi sun sha alwashin daukan matakan da suka dace, don hana shugaba Nkurunziza cika burinsa na yin sabon wa'adi na mulki.Suna masu cewa wannan mataki ya saba wa yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma tsakaninsu, wacce ta byar da damar kawo karshe yakin basasa da kasar ta yi fama da shi a farkon shekarun 2000.

Babban jami'an Amirka wanda ya gana da shugaban Burundi ya ce kasarsa za ta kakaba takunkumi kan duk wadanda za a samu da hannu wajen tayar da rigima a wannan kasa ta Tsakiyar Afirka.

A Jiya ma dai gwamnatin ta Burundi ta tilasta wa dalibai ficewa daga jami'ar kasar a wani mataki na rigakafin tashin-tashina. Sannan kuma ta toshe kafofin sa da zumunci na zamani ciki kuwa har da facebook da kuma twitter.