1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kakabawa wasu mahukuntan Tehran takunkumai

Binta Aliyu Zurmi
March 8, 2023

Amirka ta sanar da kakabawa wasu jami'an gidan yarin kasar Iran da ake zargi da take hakkin bil Adama a kan mata takunkumi, a ci gaba da bikin ranar mata ta duniya da ake yi a yau.

https://p.dw.com/p/4OPze
USA | Präsident Joe Biden
Hoto: Anna Moneymaker/Getty Images

Wata sanarwar da hukumomin Amirkan suka fidda ta ce an kuma saka wa babban kwamandan sojin kasar da wasu manyan kamfanoni gami da shugabanninsu takunkumai.

Amirka da sauran kawayenta na yammacin duniya na goyon bayan matan kasar Iran bisa cin zarafi da suke fuskanta daga wananan gwamnati da shugaba Ebrahim Raisi ke jagoranta.

Wannan dai shi ne karo na 10 da ake saka wa wasu jami'an Tehran takunkumi tun bayan mutuwar matashiyar nan mahsa Amini a hannun jami'ain gyara hali na Hisba a kasar a Satumba shekarar da ta gabata.

Ko a farkon wannan makon ma kungiyar tarayyar Turai ta sanar da wasu jerin takunkumai ga wasu mahukuntan na Tehran.