Amirka na shari'a da Volkswagen
January 4, 2016Talla
A ranar Litinin din nan mahukunta a Amirka sun bayyana a hukumance cewa sun gurfanar da kamfanin Volkswagen saboda zamba me alaka da nau'urar da ke bada bayanai marasa inganci a injinin motocin kamfanin a kasar Amirka.
A cewar mahukuntan kasar ta Amirka dai sun sami wannan na'ura da ba ta bada bayanai na gaskiya a kusan motocin kamfanin 600,000 wadanda aka sayar da su a Amirka kadai. Za dai a iya cin tarar kamfanin Dala miliyan dubu ashirin kan wannan zamba.