1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Iran ta sake tunani kafin kai farmakin fansa

Suleiman Babayo MAB
January 5, 2020

Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi gargadi kan wurare 52 da Amirka za ta kai farmaki muddun Iran ta yi tunanin kai farmakin daukan fansa.

https://p.dw.com/p/3Viya
Iran Teheran Airport Überführung Sarg von Soleimani
Hoto: AFP/Fars/H. Mersadi

Shugaba Donald Trump na Amirka ya gargadi mahukuntan kasar Iran da cewa muddun suka kuskura suka kai harin ramuwa kan kashe babban hafsan sojan kasar za su dandana kudarta, domin Amirka ta tanadi wurare 52 da za ta kai farmaki a Iran.

Wannan na zuwa yayin da a cikin kasar ake jana'izar babban hafsan sojan dakarun musamman Janar Qassem Soleimani a birnin Ahwaz na Iran wanda ya mutu sakamakon harin Amirka a birnin Bagadaza na kasar Iraki.

Lamarin ya tabarbare inda aka kai hare-haren rokoki cikin wurare masu tsananin tsaro na birnin Bagadaza da ke kasar Iraki, wajen da ke kewaye da ofisoshin jakadancin da gidajen manyan jami'an gwamnati, abin da ke nuna martani kan harin Amirka da ya janyo mutuwar jami'in sojan na Iran.