1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na janye daga Siriya

Yusuf Bala Nayaya
December 19, 2018

Kasar Amirka ta fara janye dakarunta daga kasar Siriya zuwa gida a daidai lokacin da ake bude sabon babi na yaki da mayakan IS a cewar fadar White House, wacce ta ce mayakan na IS da "daularsu" an karya lagonsu.

https://p.dw.com/p/3AOxP
Sarah Sanders Trump PK Sprecherin
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Olivier

A cewar mai magana da yawun fadar ta White House Sarah Sanders wannan nasara da aka samu kan mayakan na IS baya nufin kawo karshe na gamayyar kasashe da suka hadu inda suke yaki da IS. Sai dai a cewar ministan tsaro na Birtaniya ya kalubalanci matakin na Amirka inda ya ce batu na cewa an kawo karshen mayakan na IS a Siriya bai ma taso ba. Tobias Ellwood ya ce ba zai taba yarda da jawabin na Trump na Twitter ba. Kasancewar mayakan na IS na rikide zuwa wasu kungiyoyi wadanda babbar barazana ce ga makomar zaman lafiya a duniya.