1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta dakatar da gabilin taimakon Gabon

Suleiman Babayo ZMA
September 27, 2023

Sakamakon juyin mulkin da aka samu a kasra Gabon yanzu kasar Amirka ta katse wasu ayyukan jinkai a kasar da ke yankin tsakiyar nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/4WqaE
Gabon | Sojoji sun kwace madafun iko
Sojojin Gabon sun kwace madafun ikoHoto: AA/picture alliance

Gwamnatin Shugaba Joe Biden ta kasar Amirka ta dakatar da gabilin taimakon da bai shafi jinkai ba ga kasar Gabon sakamakon juyin mukliin da sojoji suka yi a watan jiya na Agusta wanda ke zama juyin mulki na biyu a nahiyar Afrika cikin wannan shekara.

Sakataren harkokin wajen kasar ta Amirka, Antony Blinken ya bayyana dakatar da taimakon kan kasar ta Gabon har zuwa lokacin da aka sauyin da aka samu bayan juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin tsohon Shugaba Ali Bongo, amma gwamnatin Amirka ta ce matakin ba zai shafin ayyukanta a kasar ta Gabon mai arzikin man fetur na yankin tsakiyar Afirka ba.

Haka kuma gwmnatin ta Amirka ta katse wasu ayyukan taimako a Jamhuriyar Nijar samakaon kwace madafun iko d asojoji suka yi a kasar da ke yankin yammmaci9n Afirka, aamma a hukunce gwamnaatin ta Amirka ba ta ayyana abin da ya faru a Jamhuriyar Nijar a matsayin juyin mulki ba.