1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta fita cikin masu taimakon ta'addanci

Abdul-raheem Hassan
December 14, 2020

Wanke sunan Sudan cikin kasashen da ke taimakawa 'yan tadda a duniya, na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan da gwamnatin Khartoom ta ta yi mubabaya'a da tayin Washinghton na maida huldar jakadanci da kasar Isra'ila.

https://p.dw.com/p/3mhdb
Sudan Khartum US-Außenminister Pompeo und Abdalla Hamdok
Hoto: Sudanese Government/Saudi Press Agency/picture-alliance

Matakin zai bude wa Sudan kofar samun agaji da sassaucin basussuka, tare da shigowar masu zuba jari domin farfado da tattalin arzikin kasar da ke fama da matsi, yayin da a gefe guda kasar ke fama da rikicin siyasa da annobar Corona.

Shekaru 27 kenan Amirka ta sanya kasar Sudan cikin jerin kasashen da ke tallafawa 'yan ta'dda, sai dai a watan Oktoban 2019 Shugaba Donald Trump ya yi alkwarin wanke sunan Sudan.