1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ce a gaggauta sakin Bazoum

July 29, 2023

Sakataren harkokin wajen Amirka, Antony Blinken ya bukaci a gaggauta sakin hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.

https://p.dw.com/p/4UX69
Shugaba Mohamed Bazoum
Shugaba Mohamed BazoumHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Blinken da ke kammala ziyarar aikinsa ta kasashen yankin Pacific, ya ce Amirka za ta bai wa shugaba Bazoum dukannin wani goyon bayan da yake bukata.

Babban jami'in na Amirka ya kuma yabawa rawar da shugaba Bazoum ya taka wajen wanzar da zaman lafiya, ba a Nijar kadai ba har zuwa sauran kasashen da ke yammacin Afirka.

Blinken ya ce ci gaba da tsare shugaban na barazana ga hadin kai tsakanin kasashen biyu da aka kwashi tsawon shekaru da kullawa da ma daruruwan miliyoyin tallafi ga Nijar din.

Tuni da Blinken ya gana da ministar harkokin wajen Faransa kan halin da Nijar ke ciki, inda ya jadadda bukatar gaggauta mayar da kasar kan tafarkin kundin tsarin mulkin kasar.