1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin duniya na fuskantar Barazanar

Salissou Boukari
June 1, 2018

Tatattalin arzikin duniya na fuskantar babbar barazana bayan matakin da Amirka ta dauka na kara haraji kan karafa da ta yi kan kasashe abokan huldarta da suka hada da Canada, Mexico da kasashen Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/2ykWD
Donald Trump
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/A. Harnik

Tuni dai kasashen suka soma mayar ta martani a daidai lokacin gudanar da babban zaman taron G7 kan tattalin arziki a kasar Canada. Amirka dai ta ce ta dauki matakin karin harajin ne na kashi 25 cikin 100 da kuma kashi 10 cikin 100 a fanin nau'i na karafan da ake shigarwa a cikin kasarta, domin inganta harkokinta na tsaron cikin gida. 

Sai dai wannan mataki na nuna ba sani ba sabu da shugaban na Amirka Donald Trump ya dauka, ya haifar da tada jijiyoyin wuya har ma a cikin jam'iyyarsa ta Republicain, inda shugaban majalisar dokokin Amirka Paul Ryan ya ce wannan mataki ya shafi abokan huldarsu wadanda ta kamata su yi aiki tare domin inganta harkokin kasuwanci da ya sabawa ka'ida da kasar China ke yi. Kasar Canada dai na a matsayin ta farko da ta sanar da mayar da martani na saka haraji kan kayayakin na Amirka.