1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadar White House na turjiya ga kwamitin bincike

Abdoulaye Mamane Amadou
October 9, 2019

Fadar gwamnatin Amirka ta yi fatali da duk wani bayar da hadin kai game da batun ci gaban da ake na binciken shugaban kasar Donald Trump wanda hakan kan iya kai ga daukar matakin tsige shi daga mulki.

https://p.dw.com/p/3QvM6
USA Weißes Haus in Washington mit Stoppschild
Hoto: Getty Images/AFP/K. Bleier

Lauyan da ke kare Donald Trump ya bayyana a cikin wata wasikar da ya aikewa kakakin majalisar dokokin Amirka Nancy Pelosi cewa, ci gaba da binciken da 'yan jam'iyyar Demokrats ke hankorin yi kan batun matsin lambar da ake tuhumar shugaba Trump yayi ga takwaransa na Ukrain, domin ya binciki abokin hamayyarsa Joe Biden don samun wata dama ta daukar matakan tsige shugaban, baya da wani tushe da daga kundin tsarin mulki.