1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisa ta shiga shirin tsige Trump

Ramatu Garba Baba
September 25, 2019

Shugaba Donald Trump zai fitar da bayani a wani yunkurin kare kansa daga zargin da ake masa na kokarin tursasa shugaban kasar Ukraine don cimma wata manufar siyasa.

https://p.dw.com/p/3QCUL
Donald Trump
Hoto: Getty Images

Shugaba Donald Trump ya yi alkwarin gabatar da wata takarda a game da tattaunawar da suka yi da shugaban kasar Ukraine Volodymr Zelensky ta wayar tarho, batun da yanzu ya kai ga matsin lamba daga bangaren jam'iyyar adawa ta Demokrat na son ganin an kaddamar da shirin tsige shugaban.

An dai zarge shi da laifin matsawa Shugaba Zelensky da ya gabatar da bincike na rashawa akan dan Joe  Biden tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda ake ganin ya yi ne a matasayin bita da kullin siyasa kan babban abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasar na shekara mai zuwa. Trump dai ya musanta zargin sai dai majalisa na cewa matakin ya keta haddin kundin tsarin mulkin kasar.