Amirka na kalubalantar Koriya ta Arewa
April 28, 2017Talla
Rex Tillerson ya bayyana haka ne gabannin wata tattaunawa da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar a kan Koriya ta Arewa. Gwamnatin Donald Trump wacce tun farko ta dage a kan matsayin yin amfani da karfin soji a kan Koriya ta Arewa, a yanzu ta sassauto, domin bin hanyoyin diplomasiya don warware takaddamar.