1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na bukatar a binciki Rasha

Binta Aliyu Zurmi
February 23, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ya bukaci da a gudanar da bincike kan wasu bayyanan sirri da aka bankado daga Rasha na kokarin da take yi na tsoma hannunta a harkokin yakin neman zaben shugaban kasar da za a yi a bana.

https://p.dw.com/p/3YFjW
Japan Osaka | G20 Gipfeltreffen - Donald Trump und Vladimir Putin
Hoto: pictura-alliance/dpa/Tass/M. Metzel

Trump ya ambata hakan ne ga manema labaru a Fadar White House a lokacin da ya ke shirin kai ziyara kasar Indiya, inda ya ce ba a sanar da shi hakikanin abubuwan da bayanan suka kunsa ba, musamman a kan yakin neman zaben Mr. Sanders.

A gefe guda kuma shugaban na Amirka ya taya abokin hamayar sa murnan lashe zaben fidda gwani na jihar Nevada.

Ana dai zargin Rasha da yunkurin yada wasu labarai mara kan gado da ma wasu nauika na farfaganda a zaben na Amirka da ke tafe.