Amirka ta zarce kasashe wajen yawan wadanda suka mutu
April 14, 2020Talla
Jami'ar John Hopkins wacce ta bayyana alkaluma ta ce ya zuwa yanzu Amirka ita ce kasar da ta fi kowacce samun yawan mutane da suka mutu kimanin dubu 23 da 'yan ka tun lokacin da annobar ta barke, yayin da wasu mutane dubu 550 ke dauke da kwayoyin cutar. Shugaba Donald Trump ya ce za su kara yawan gadajen karbar masu jinya a cikin asibitoci da kuma daukar karin matakai domin shawo kan cutar.