1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Majalisa ta tabbatar da zaben Joe Biden

January 7, 2021

Majalisar dokokin Amirka ta amince da zaben da aka yi wa Joe Biden a matsayin shugaban kasa, batun da ya ake ganin ya kawo karshen turka-turkar kan zabukan kasar.

https://p.dw.com/p/3ncjR
USA | Joe Biden designierter Präsident | Rede in Wilmington
Hoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Bayan zaman da suka yi na hadin gwiwa, majalisun dokokin Amirka sun amince da nadarar da Joe Biden ya samu a zaben shugaban kasa da ya gudana a watan Nuwamban bara. 

Tun da fari dai zaman na majalisun ya hadu da tarnakin magoya bayan shugaba Donald Trump da ya sha kayi a zaben, kafin daga bisani bayan sa'o'i kalilan a cigaba da shi.

Majalisar Dinkin Duniya gami da kasashen da ke fada a ji a fadin duniya da suka hada da China da Jamus, suka bayyana abin da ya faru  a matsayin karan tsaye ga demokaradiyya.