Biden ya lashe zaben jihohin Texas da Massachusetts
March 4, 2020Talla
A sama da jihohi goma na zaben share-fage na jam'iyyar hamayya ta Demokrats, tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden ya samu nasara, inda a Texas ya doke Bernie Sanders da kuma Elizabeth Warren a Jihar Massachusetts. A shirye-shiryen fitar da gwanin dan takarar da zai fafata da Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican mai mulki a zaben watan Nuwambar bana. Joe Biden ya ce wannan wata alama ce ta kawo karshen mulkin Donald Trump a Amirka.