1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar Koriya ta Arewa za ta aike da makamai Rasha

Binta Aliyu Zurmi
June 13, 2023

Ma'aikatar cikin gida a Amirka ta nuna damuwa a kan yiwuwar Koriya ta Arewa ta aike wa Rasha da makaman yaki.

https://p.dw.com/p/4SUxH
USA Washington | Rede Joe Biden nach Ende des Schuldenstreits
Hoto: Jim Watson/AFP

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da shugaba Kim Jong Un ya bayyana goyan bayan Pyongyong ga Kremlin a yayin da suke bikin ranar hadin kan kasa.

A baya ma dai Amirka ta zargi Koriya ta Arewa da aike wa sojojin Wagner da makamai, sai dai Koriya ta musanta wannan zargin.

Ana ganin dai fitowar da Shugaba Kim ya yi a karon farko ya nuna wa duniya akwai wata alaka tsakanin shi da Rasha na zama wani abun damuwa musamman ma a wannan yakin da take yi da Ukraine.