1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Daukar matakan bai daya a kan Rasha

January 25, 2022

Kasashen Turai sun sami goyon bayan Amirka na daukar matakan bai daya a kan kasar Rasha bisa barazanar mamayar Ukraine da ake zarginta da yi.

https://p.dw.com/p/462Gx
Symbolbild Ukraine Konflikt Videogipfel Biden
Hoto: The White House/AP/picture alliance

Shugaban Amirka Joe Biden ya ayyana goyon bayan shi dari bisa dari ga kasashen yamma a kan daukan mataki na bai daya ga mahukuntan Rasha a yunkurin da su ke yi na mamayar Ukraine.

Mr Biden ya bayyana haka ne ga manema labarai jim kadan bayan wata tattaunawa da ya yi ta kafar bidiyo da shugabannin kasashen Turai gami da na kungiyar tsaro ta NATO. 

Amirka ta ce rundunar dakarunta dubu 8500 na zaman jiran ko ta kwana da za a tura su domin taimakawa dakarun NATO.

A nashi bangaren shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz cewa ya yi shawara ta rage ga Rasha na janye duk wani yunkuri da take da shi a kan Ukraine.

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya tabbatar tun a baya da ba shi da niyyar mamayar Ukraine amma kuma ya jibge sojoji dubu dari dab da kasar.