1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Amirka da Iran na kara zafi

Gazali Abdou Tasawa
September 17, 2019

Kasashen duniya na ci gaba da nuna fargaba game da yiwuwar barkewar yaki tsakanin Amirka da Iran, bayan hare-haren da aka kai kan cibiyoyin hakar man fetur na kasar Saudiyya.

https://p.dw.com/p/3Phid
BG Geschichte Iran USA Konflikte US Hubschrauber eskortiert Tanker im Golf von Dubai
Hoto: picture-alliance/dpa

Tuni dai kungiyar 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka dauki alhakin kaiwa wadannan hare-haren, sai dai Amirka da Saudiyya na zargin Iran da kai hare-hare, zargin da mahukuntan Tehran din suka musanta.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan wani taro da ya gudanar a Litinin din da ta gabata da mukarrabansa inda suka yi nazarin halin da ake ciki da kuma matakan dauka, Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayyana hare-haren da aka kai Saudiyyan a matsayin gagarimin harin da ya kamata kasarsa ta mayar da martani mai karfi.

Sai dai babban sakataren kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty International Kumi Naidoo ya yi gargadin cewa duk wani matakin soja da Amirka za ta dauka kan Iran, zai kara dagula al'amura ne kawai a yankin Gabas ta Tsakiya.