1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar muzgunawa al'ummar kasar Yuganda

Binta Aliyu Zurmi
February 7, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da Amirka sun nuna damuwa kan yadda jami'an tsaro a kasar Yuganda ke gallazawa al'umma musamman ma fararen hula.

https://p.dw.com/p/46eOf
Flaggen USA und EU
Hoto: AP

A wata sanarwa da ta fidda, EU ta nuna damuwa kan muzgunawar da jami'an tsaro ke yi wa mutanen da suka hada da masu rajin kare hakin al'umma da 'yan adawa da kuma ma masu rajin kare muhalli. 

Ita ma dai Amirka a wani sako da ta fidda a makon jiya ta nuna damuwa kan karuwar bacewar mutane da ma yadda jami'an tsaro ke azabtar da al'umma, na baya-bayan nan shi ne yadda aka kame wani marubuci dan kasar aka kuma tsare shi na tsawon lokaci ana azabtar da shi bisa wani rubutu da ya yi da ke nuna gazawar gwamnatin Museveni. 

Amirka ta ce hakan na kara yin tabo a kan mulkin Shugaba Yoweri Museveni wanda ke kan karaga mulki tun a shekarar 1986.