Amincewa da dokar haramta takara a Masar
April 24, 2012Hukumomin mulkin soja na Masar sun rattaɓa hannu kan dokar da ke haramta ma waɗanda aka damawa da su a lokacin mulkin Hosni Mubarak tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa. Wannan dokar ta shafi waɗanda suka taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙasa, ko mataimakin shugaba, ko ma dai firaminista, shekaru 10 kafin awan gaba da guguwar neman sauyi ta yi da kujerar mulkin Mubarak. Kana wannan doka ta haramta wa mambabin kwamitin ƙoli na jam'iyar da ta shafe shekaru ta na riƙe mulkin Masar tsayawa takara. Ɗaya daga cikin waɗanda wannan mataki zai yi tasiri kansa, shi tsohon firaminista Ahmed Chafiq.
A ranakun 23 da kuma 24 ne za a gudanar da zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa a Masar. Sai dai kuma har yanzu majalisar sojoji da ke tafiyar da mulki ba ta samar wa ƙasar da sabon kundin tsarin mulki kamar yadda ta alkawarta ba. Lamarin da ke haddasa shakku tsakanin ɓangarori na ƙasar game da aniyarsu ta wanke hannaye daga madafun iko a watan yuli mai zuwa idan Allah ya yarda.
Mawallafi: Mouhamadaou Awal
Edita: Umaru Aliyu