1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da Soji akan Libiya ya mamaye taron Turai a Brussels

March 24, 2011

Shugabannin ƙasashen Turai na ƙokarin shawo kan rarrabuwar kawunansu kan matakin Soji akan Libiya.

https://p.dw.com/p/10h5d
Hoto: AP

A taron kwanaki biyu da aka buɗe a yau a birnin Brussels, shugabannin Turai na fatan sasanta saɓanin da ke tsakaninsu kan matakin sojin da aka ɗauka akan Libiya. Rarrabuwar kawuna akan ƙudurin na Majalaisar Ɗunkin Duniya akan Libiyan dai, ya mamaye Taron. Faransa tace hare-haren kawancen akan Libiya zai iya ɗaukar makonni nan gaba, a yayin da Britaniya ta sake kira ga ƙungiyar tsaro ta NATO da ta ɗauki jagorancin hare-haren ƙawancen akan Libiya.

Tripoli dai na cigaba da fuskantar lugudan boma-bomai da makamai masu linzami a rana ta shida da jiragen yaƙin kawancen ƙasashe suka afkawa ƙasar da ƙarfin so. A daidai lokacin da ƙungiyar tsaro ta NATO ke shirin karɓar ragamar shugabancin wannan hari akan Libya. Majiyar diplomasiyya na nuni da cewar, Turkiyya ce a gaba wajen ƙin amincewa NATO ta jagoranci wannan gamayya, tare da kira ga Britaniya, Faransa da Amurka dake aiwatar da dokar haramta shawagin sararin samaniyan Libyan, dasu dakatar hare-haren da suke kaiwa. Jiragen yaƙin kawancen dai sun kwana suna kai hari a cikin Libiyan, sai dai sun gaza hana Tankuna yaƙin dakarun Gaddafi sake shiga Garin Misrata, inda suka karɓe madafan ikon babban Asibitin garin. Rahotanni na nuni da cewar 'yan Tawayen Libyan na na kokarin shiga garin Ajdabiya, a ƙokarinsu na karɓe wannan birni da ke yankin gabashi mai arzikin man Petur daga Dakarun da ke maraya Gaddafi baya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Ahmad Tijjani Lawal