1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da bamabamai masu tarwatsewa a yaƙin Libiya

Tijani LawalApril 18, 2011

Ana zargin sojojin Gaddafi dai laifin amfani da muggan bamabaman nan masu tarwatsewa domin su haɗa da na nesa, musamman a fafatawar da ake yi akan garin Misrata

https://p.dw.com/p/10vdx
Harsashin bamabamai masu tarwatsewa da aka ce ana amfani da shi a yaƙin LibiyaHoto: AP/Human Rights Watch

Rahotanni dai na nuni da cewar mayaƙan na Gaddafi suna amfani da waɗannan nakiyoyi masu tarwatsewa akan fararen hula da gine-gine, inda har aka gabatar da hotunansu da ke tabbatar da hakan. Wani rahoton da wani ɗan Jaridar New York Times ya  rubuta daga wannan birni dake da nisan kilomita 200 daga babban birnin Libya na Tripoli, na bayyana yanayin waɗannan nakiyoyi masu lahani.

Kazalika wani likita dake garin na Misrata ya shaidarwa gidan talabijin na Aljazeera, irin asarar rayuka da ya gane ma idanunsa sakamakon harin da wadannan nakiyoyi masu tarwatsewa:

"Ni da abokin aiki na, mun gani da idanummu yawan mutanen da suka samu raunuka  sakamakon waɗannan nakiyoyi, daga cikinsu har da wani ɗan jarida mai ɗaukar hoto na Farasnsa. Da yawa daga cikin waɗanda harin nakiyoyin ya rutsa da su yara ne ƙanana, wadanda suka raunana a ƙirji, ciki da idanu."

Babu wasu cikakkun alƙaluma da aka bayar

Kawo yanzu dai babu cikakken adadin waɗanda suka rasa rayukansu ko kuma jikkata daga hare-haren nakiyoyi masu tarwatsewar da ake zargin dakarun Gaddafi da amfani dasu akan fararen hula a Misrata.

Gwamnatin Muammer Gaddafi a Tripoli dai ta ƙaryata wannan zargi, tare da nuna takaicin yadda ƙasashen ƙetare da ma ƙungiyoyin taimako ke amincewa da dukkan abin da 'yan tawaye suka faɗa ba tare da sauraron ɓangaren gwamnati ba. Mussa Ibrahim shi ne kakakin gwamnatin na Libya:

"Muna takaicin yadda  waɗannan ƙungiyoyi ba sa jin kiran da muke yi a garesu zuwa birnin Tripoli, don kafa ofisoshinsu kana su je Misrata su gane wa idanunsu abin dake faruwa. A maimakon haka sun gwammace su saurari maganganu ta waya, da irin rahotannin da mayaƙan tawaye ke gaya musu, kuma su amince da su. Muna takaicin waɗannan bayanai waɗanda ba gaskiya ba ne."

'Yan tawaye na fafutukar kame garin Al-Braga

Libyen Rebellen Ajdabiya Munition
'Yan tawayen Libiya dake fafutukar mayar da Al-Brega ƙarƙashin ikonsuHoto: dapd

Kusan wata guda ke nan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartar da aiwatar da ƙudurin nan na haramta wa jiragen Gaddafi yin zirga-zirga a sararin samaniyar Libiyan. A daren lahadi zuwa da rana dai 'yan tawayen sun ci gaba da fafutukar mallakar garin Al-Brega mai albarkatun man fetur dake yankin gabashin Libiyan.

A wannan fafutuka dai a cewar rahotannin gidan talabijin ɗin Aljazeera, 'yan tawayen sun yi asarar rayukan mutane shida, ayayinda wasu 20 suka jikkata. Akwai dai dakarun Gaddafi a tsakiyar birnin, ayayinda kewayensa ke ƙarƙashin ikon 'yan tawayen.

'Yan tawayen na amfani da rigunan sulke

 A karon farko dai an ruwaito cewar mayaƙan 'yan tawayen suna sanye da rigunan sulke da zai iya karesu daga harin bomb, waɗanda ake ganin cewar sun samo asali ne daga Britaniya da Qatar. Kuma akwai alamun na'urorin sadarwa na taurarin ɗan Adam a tare da 'yan tawayen.

Libyen Aufständische bei Brega
'Yan tawaye a wajen garin Al-BregaHoto: dapd

Neman madafan iko akan  Al-Brega mai arzikin mai  dake da yawan mutane dubu 100, ya sa garin ya zame wurin tserewa ga waɗanda ke da ƙarfin hakan, kasancewar ya zame filin daga tsakanin dakarun Gaddafi da na 'yan tawayen Libiyan.

Mawallafa: Peter Steffe/Zainab Mohammed Abubakar

Edita: Ahmad Tijani Lawal