Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Sudan
August 31, 2020Talla
Sabbin alkaluman da hukumomin kasar suka fitar sun kuma nunar da cewa akwai wasu mutum 44 da ke kwance a asibitoci sakamakon ambaliyar.
Kazalika akwai gidaje sama da dubu 37 da wasu gine-ginen gwamnati 150 da ruwan na sama ya lalata.
Sudan din dai ta saba samun ruwan sama mai karfi cikin watannin Juni zuwa Oktobar kowace shekara, wanda galibi ke haddasa ambaliya.
Arewacin yankin Darfur da kuma jihar Sennar da ke kudancin kasar dai na daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi yi wa lahani.