1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 341 a Chadi

September 10, 2024

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa mace-macen sun faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliya da ake ta tafkawa a kasar Chadi, yayin da wasu mutanen sama da miliyan 1.5 suka rasa muhallansu.

https://p.dw.com/p/4kRvj
Wasu mazauna N'djamena da ke kokarin kwashe kayansu sakamakon ambaliyar ruwa
Wasu mazauna N'djamena da ke kokarin kwashe kayansu sakamakon ambaliyar ruwa Hoto: Mahamat Ramadane/REUTERS

Ofishin kula da jinkai na MDD ya ce ambaliyar ruwan ya shafi larduna 23 na kasar ta Chadi. Kazalika gidaje sama da 164,0000 suka lalace tare da asarar shanu sama da dubu 70,000.

Karin bayani: Ambaliya ta yi barna a Chadi 

Har yanzu dai hukumomin kasar ta Chadi  ba su fitar da alkaluman wannan ibtila'i ba, wanda ko a makon da ya gabata ambaliyar ruwan ta halaka wasu daliba 14 tare da malaminsu a yankin Ouadda da ke shiyyar gabashin kasar. Wasu rahotannin sun bayyana cewa mutane 54 sun mutu a lardin Tibesti da ke da tsakiyar sahara a arewacin kasar sakamakon mamakon ruwan sama.