1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen ambaliyar ruwa a Agadez

Salissou Boukari
August 15, 2018

Birnin Agadez da ke a matsayin birni mai tarihi kamar yadda hukumar raya al'adu ta duniya ta UNESCO ta ayyana wasu mahimman wuraran tarihi na birnin, na fuskantar babban kalubale na ambaliyar ruwan sama.

https://p.dw.com/p/33EKJ
NO FLASH Überschwemmung Afrika Kenia Fluss Katastrophe Flut
Hoto: picture alliance/Photoshot

A cewar Magajin garin birnin na Agadez Rhissa Feltou, matsalar ta yi kamari, inda ko a wayewar garin wannan rana ta Laraba ambaliyar ruwan ta awon gaba da wata motar agajin gaggawa ta gundumar Tabelot dauke da mutane biyar a cikinta a wajejen Dabaga da ke a nisan kilo mita 45 daga birnin Agadez.

Birnin na Agadez da ke da al'ummar da yawanta ya kai mutum 145.000, na fuskantar babbar barazana ne daga wata babbar hanyar ruwa ta Telwa wadda ruwan da ke gangarowa daga duwatsu na Air ta kwarara a cikinta a cewar Magajin garin na Agadez, inda ya ce tuni ambaliyar ta yi awon gaba da garake, gidaje da kuma dabobi masu tarin yawa.

Babban abun da yanzu ake gudu shi ne idan abun ya ci gaba ba tare da wani mataki ba, hakan ka iya janyo bacewar birnin na Agadez a cewar hukumomin.