1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta yi ɓarna a Zimbabwe da Burundi

Usman ShehuFebruary 11, 2014

Wannan ambaliya da ta shafi dubban mutane, ta sa ƙasashe kamarsu Zimbabwe neman agaji daga ƙasa da ƙasa domin ceto waɗanda wannan masifar ta shafa.

https://p.dw.com/p/1B73s
Mosambik Überflutung
Hoto: Getty Images

A cewar sakataren ƙungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross Anselme Katiyunguruza da ke birnin Bujumbura, yace ma'aikatansu sun kwaso gawarwakin mutane tsakanin 60 izuwa 70. Ruwan saman dai an yi shi ne tun a shekaran jiya Lahadi (09. 02. 14), inda ya haddasa koguna uku suka tumbatse, abin da kuma ya sa ruwa ya malalo izuwa Bujumbura, babban birnin ƙasar ta Burundi.

Hakama a Zimbabwe

A wani labari makamancin wannan, hukumomin ƙasar Zimbabwe sun ƙaddamar da asusun neman taimako, domin tallafawa dubban mutane da ambaliyan ruwa ta yi wa ɓarna. Al'ummomi da ke kusa da wani tabki da ake ginawa a yanzu haka a kudancin ƙasar, su ne suka fi shiga matsala sakamakon ambaliyan da aka yi. Gwamnati a Harare ta ce tana buƙatar dalar Amirka miliyan 20, domin sakewa waɗanda ke fiskantar hatsari mastuguni, dkana kuma a ceto waɗanda yanzu haka ruwan ya yi awun gaba da gidajensu. Kawo yanzu dai gwamnatin Robert Mugabe ta yi na ta ƙoƙarin, inda aka tsugunar da waɗanda lamarin ya shafa a makarantu da sauran sansanonin da aka tanardar, amma dai har yanzu ana buƙatar tallafi daga ƙasashen waje domin munin lamarin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Saleh Umar Saleh