1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alƙawarin Merkel kan rikicin kuɗin Girka

August 24, 2012

Angela Merkel ta ce za ta yi tsayuwar daka domin ganin cewar Girka ba ta daina amfani da kuɗin Euro ba. Bayanin na ta ya zo ne bayan ganawa da ta yi da firaministan Girka a Berlin.

https://p.dw.com/p/15wTd
Der griechische Ministerpräsident Antonis Samaras wird am Freitag (24.08.2012) von Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) vor dem Bundeskanzleramt in Berlin begrüßt. Thema des Treffens ist das weitere Vorgehen in der Euro-Schuldenkrise. Foto: Kay Nietfeld dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi alkawarin taimaka wa Girka warware matsalar karancin kudi da ke addabarta. Bayan da ta gana da firaministan na Girka Antonis Samaras a birnin Berlin, Merkel ta ce za ta yi iya kokarinta domin kasar ta ci gaba da zama cikin rukunin kasashen Turai da ke amfani da Euro. Sai dai ta nemi bakon na ta ya aiwatar da daukacin matakan tsuke bakin aljuihu da aka gindaya wa Kasar ta Girka.

Ko da shi ke dai Samaras ya ce kasarsa a shirye ta ke ta bi ka'idojin na kasashen duniya sau da kafa, amma dai a cewarsa Girka na bukatar karin lokaci kafin ta aiwatar da sauye sauyen tattalin arziki musamma ma matakin nan na ci gaba da tsuke bakin aljuhu. Ko da ita ma Merkel sai da ta bayyana cewar kasar ta Girka na bukatar sararawa kafin ta dora kan inda ta tsaya a yunkurinta na tsumi da tanadi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi