1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar jihar Kano sun fara Azumi cikin fargaba

July 20, 2012

Halin da ake ciki na rashin tsaro ya dauki hankali a daidai lokacin da al'ummar musuli a Najeriya suka tashi da Azumi na watan Ramadan

https://p.dw.com/p/15caM
Hoto: picture-alliance/dpa

Ayayin da aka fara azumi ayau alummar jihar Kano a Najeriya sun fara azumin cikin fargaba da matsanancin yanayi inda mutane ke kokawa bisa karancin kudi da kuma zaman dar dar na abin da ka iya faruwa.a jiya ne dai wasu mutane akan babura suka kai farmaki rukunin masana antu na Sharada a jihar ta kano,wanda yayi sanadiyyar rasuwar mutane hudu.

Alummar jihar Kano sun fara azumin bana cikin wani yanayi matsananci sakamakon zaman dar dar da kuma karancin kudi ahannun jama a,wanda ya haddasa rashin ciniki da kuma kara jefa jama'a a cikin mawuyacin hali.a yammacin alhamis din nan ne wasu mutane akan babura suka kai farmaki unguwar Sharada dake birnin inda suka harbe wasu mutane uku daga bisani kuma aka kara kai wani farmakin a unguwar Hotoro inda nan ma aka sami asarar rai, koda yake kakakin rundunar yansandan jihar rasuwar mutane uku ya tabbatar, wannan hari ya kara jefa al'ummar jihar cikin fargaba baya ga matsananciyar wuyar rayuwa da ake fama da ita a jihar, sakamakon kukan da al'umma keyi na rashin kudi. Babaywale dake zaman masanin tattalin arziki a jihar Kano ya bayyana cewar jihar Kano ta dade bata fuskanci tsananin rayuwa irin wannan lokaci ba.

Abdulrazak Isa dan kasuwa ne dake sayar da kayan masarufi a jihar ta Kano yace ko kadan bana babu ciniki, domin a bara yakan yi cinikin miliyan guda kowacce rana amma a bana da kyar yake hada cinikin naira dubu dari uku akallum. Ahmad Braza shine jami'in hulda da jama'a na kungiyar masu sayar da kayan marmari a jihar Kano. Yyace cinikin bana sai dai kawai ayi kurum, amma batun ciniki sai dai hakuri. Malam Abubakar dattijo ne a jihar Kano ya bayyana cewar batun kudi sai dai hakuri, domin kullum lamura kara Ta'azzara suke yi.

Ramadan in Deutschland
Shirin buda-baki a JamusHoto: picture-alliance/dpa

Duk da cewar yan kasuwa na cewar an sami ragin farashin kayyaki abana amma duk da haka ana kokawa saboda rashin ciniki, kasancewar galibi babu kudi a hannun alumma.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango

Edita: Umaru Aliyu