1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umar Siriya na fatan ganin an ɗauki wani mataki kan mahukuntan ƙasar

August 2, 2011

A yayinda al'umar Siriya ke fatan ganin Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauki wani sahihin mataki kan mahukuntan ƙasar, a ɗaya hannun sojoji na ci gaba da kai farmaki kan masu zanga-zangar adawa da gwamnati

https://p.dw.com/p/129lX
Masu zanga-zanga sun cunna ƙyandura a titunan Siriya dangane da watan RamalanaHoto: PA/abaca

Dubban-dubatar 'yan Siriya ne suka shiga fafutukar neman tsira da rayukan su a yayin da dakarun gwamnatin ƙasar suka yiwa garin Hama diran mikiya a ƙarshen mako a ƙoƙarin da shugaban ƙasar ta Siriya Bashar Assad ke yi na ci gaba da riƙe madafun iko da kuma daƙile masu boren adawa da gwamnatin sa. Ƙungiyoyin kare haƙƙin jama'a dai sun bayyana cewar kimanin mutane 140 ne suka mutu a lokacin farmakjin, wanda a cewar su ya sa adadin waɗanda suka mutu tun bayan ɓarkewar boren nuna adawa da gwamnatin a tsakiyar watan Maris ya kai mutane 1,400, abinda kuma a cewar Najib Ghadbia, masanin harkokin siyasar Siriya dake jami'ar Ankansas na ƙasar Amirka, a yanzu 'yan Siriya na fatan ƙasashen duniya za su sake tunani akan lamarin:

"Haƙiƙa matasan ƙasar Siriya sun zura ido suna kallon matakan da alummomin ƙasa da ƙasa za su ɗauka kuma matsayar da ƙasashen duniya za su ɗauka ne zai ƙarfafa musu gwiwa. Mun yi amannar cewar hukumomin Siriya suna ganin rashin ɗaukar mataki daga ɓangaren ƙasashen duniya wani lasisin basu damar ci gaba da yin kissa ne."

SCHLECHTE QUALITÄT SCREENSHOT Syrien Hama Gewalt Feuer Rauch Demonstrationen
Farmakin sojoji a Hama ta SiriyaHoto: picture alliance/dpa

Sai dai duk wani yunƙurin zartar da ƙudiri akan ƙasar ta Siriya a lokacin zaman kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya yana fuskantar turjiya daga ƙasashen Rasha da China, waɗanda ke da kujerun din din din a cikin kwamitin, kana suke gudun sake maimaita kutsen sojin da wasu ƙasashen suka yi a cikin Libiya ta hanyar ƙafa hujja da tanadin ƙudirin da kwamitin sulhun ya zartar- da sunan shiga tsakani na soji. Hakanan wasu ƙasashen da basu da wakilci da din din din a cikin kwamitin irin su Afirka Ta Kudu da Lebanon da India ma suna yin adawa da ƙudirin da za'a ɗauka akan ita gwamnatin Siriya., saɓanin ƙasashen Turai dake da wakilcin, ciki kuwa harda Jamus, waɗanda a cewar jakadan ƙasar ta Jamus Miguel Berger a majaisar buƙatu huɗu ke gaban su akan rikicin na Siriya:

"Kawo ƙarshen tashe-tashen hankula, sakin fursunonin siyasada kuma komawa akan tattaunawar siyasa, sa'annan da gudanar da bincike na haƙika akan abubuwan da suka faru a lokacin rigingimun."

Wannan matsayin ya tada ayar tambayar ko bukatun wasu mambobin kwamitin sulhun na haƙiƙa ne, kuma ko zartar da ƙudiri zai sa matakin soji ya biyo baya?

Volkhard Windfuhr, ƙwararre akan sha'anin yankin Gabas Ta Tsakiya dake aiki da mujallar Der Spiegel a nan Jamus ya amsa da cewar ba haka batun yake ba:

"A'a! Ina ganin babu yiwuwar afkuwar hakan. Bana jin gwamnatin Jamus da ƙungiyar tarayyar Turai da kuma Amirka za su cimma dai daiton baiwa kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya damar amincewa da sakin layi na shidda, dake zaman ƙudirin shiga tsakani ta hanyar soji - kwatankwacin na Libiya ba. Baya ga hakama, ina ganin kamar dai na Libiya, sai ƙungiyar Larabawa ta buƙaci hakan gabannin ɗaukar matakin."

A yayin da ake ci gaba da yin taƙaddama akan irin martanin daya dace ƙasashen duniya su ɗauka akan Siriya, wasu ƙwararru na yin marhanin da duk wani matakin da ba zai yi mummunan ta'asiri akan al'ummar Siriya ba, ciki kuwa harda janye jakadun ƙetare da kuma taimakawa 'yan adawa.

Mawallafi: Julia Hahn/Saleh Umar Saleh

Edita: Ahmad Tijani Lawal