1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umar Masar ba zasu daina bore ba har sai sun ga abin da ya ture wa buzu naɗi

November 23, 2011

Duk da alkawarin miƙa mulki ga farar hula a tsakiyar shekara mai zuwa da sojojin masar suka yi, duban dubatan masu bore a ƙasar sun ce sunanan kan bakarsu ta ci gaba da zaman dirshan, har sai sojojin sun bar madafan iko

https://p.dw.com/p/13FNo
Shugaban hukumar mulkin riƙon ƙwarya ta soja Mohamed Hussein TantawiHoto: dapd


A cikin wani jawabin da yayi wa al'umar ƙasa Field Marshal Tantawi shugaban hukumar wucin gadin sojin Masar yayi nuni da cewar a shirye suke da su bar madafan iko nan take idan an yi ƙuri'ar jin ra'ayin 'yan ƙasar. Wannan bayani nasa dake da tufka da warwara, ya sake fusata masu bore a ƙasar, yadda waɗanda a da ke cikin gidajensu suka sake fiffitowa kan tituna da filayen da ake zaman dirshan, abin bai tsaya a dandalin Tahrir ba, har ma da garuruwan Iskandariyya da Mansura da Damanhor da Isma'iliyya, inda mutane biyu suka halaka yayin arangama da jami'an tsaro.


A dandalin Tahrir, cibiyar masu boren, dandalin ya ruɗe da ƙarar jiniyar motocin asibiti game da sowar nuna rashin amincewa da jawabin da shugaban hukumar wucin gadin ta sojan yayi.

Ägypten Demonstrationen
Masu bore a dandalin TahrirHoto: dapd


“Mun zo nan ne don muga bayan mulkin soji a ƙasar nan, sannan a kafa hukumar farar hula da za'a zaɓeta daga wannnan dandali”


Ita ma ƙungiyar gamayyar samarin juyin juya hali, ta mayar da martini kan bayanin kamar haka:


“Muna sanar da aniyarmu ta tunɓɓuke wannan mulkin sojan da illahirin tarkacensa, kuma a shirye muke da a ƙara samun waɗanda zasu yi shahada daga cikinmu,har sai munga juyin juya halinmu yayi nasara”


A ta wani gefan kuma wasu daga cikin ƙananan hafsoshin sojan, sun ce ba sa tare kwamandodin nasu, inda su ma suka hallara a dandalin don ƙara ƙarfafa guiwar masu boren.


A can garin Bor Sa'id ma yadda samarin ke cike da fushi da jawabin da suka ce yayi biris da jajantawa waɗanda jam'an tsaro suka halaka da kuma yin kira dasu dakatar da harba musu hayaƙi mai sa kwalla da albarusan roba. An yi ta ɗauki ba daɗi da masu boren da jamian tsaro. Wani ɗaya daga cikin masu boren ma dai cewa yayi:

Ägypten Reaktionen nach dem Regierungsrücktritt
Ɗaya daga masu ta da ƙayar baya lokacin hira da Deutsche Welle a AƙahiraHoto: Amira Rahman


“Dama haka mulkin kama karyan soja yake, irin wanda Tantawi ke jagoranta, suna tsammanin tarzoma da amfani da ƙarfin tuwo zai iya tankwara mu kamar yadda hamɓararriyar gwamnati ta yi zato.”


Su kuwa jam'iyun siyasa da ke cike da ɗaukin yin zaɓe murna suka nuna da jawabin, sai dai murnan tasu bata hana su yin kira da a dakatar da ayyukan tarzoma kan masu zanga zangar neman sauyi a yankunan ƙasar ba, suna masu cewa, babu ta yadda za a samu sahihin zaɓe matuƙar al'amura ba su lafaba.


Mawallafi: Mahmoud Yaya Azare

Edita: Ahmad Tijani Lawal