1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alpha Omar konare ya kiri hukumomin Sudan su gaggauta amincewa da karɓar tawagar shiga tsakani ta Majalisar Ɗinkin Dunia

May 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bux3

Sakataran zartaswa na ƙungiyar taraya Afrika, Alpha Omar konare, yayi kira ga gwamnatin Sudan, da ta gaggauta amincewa, da karbar tawagar sojojin Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur, domin tabbatar da yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kai, tsakanin yan tawayen yankin, da Gwamnatin Khartum ,ranar 5 ga watan da mu ke ciki.

Alpha Omar konare, yayi wannan kira yau, tun daga birnin London ,inda ya gana da Praminsita Tony Blair, a game da batun.

Muddun, damana ta fara, ba tare da an tura wannan runduna ba,inji shi, to za a fuskanci koma baya, a dangane da yunƙurin shimfiɗa da zaman lahia a yankin Darfur.

A yau, wasu wakilan majalisar Ɗinkin Dunia, 2, sun sauka a birnin Khartum,, domin tantanawa da hukumomi, a kan matakan aika rundunar.

A na sa ɓangare shugaban adawa, Hasan El Turabi, ya bayyana cewar, yarjejeniyar da aka cimma, a birnin Abuja, gaba ɗayan ta, na ƙunshe da kura-kurai.