1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Adadin sojan Burkina Faso da suka mutu sun karu

Abdoulaye Mamane Amadou
November 15, 2021

Hukumomi a Burkina Faso sun tabbatar da karin adadin sojan kasar da suka mutum, biyo bayan mummunan hari da 'yan ta'adda suka kai.

https://p.dw.com/p/432ON
Symbolbild I Sicherheitsbeamte Burkina Faso
Hoto: Ahmed Ouoba/AFP/Getty Images

Adadin sojojin da suka gamu da ajalinsu a wani harin ta'addanci a Burkina Faso sun haura zuwa 32. Tun daga farko dai hukumomin kasar ta Burkina Faso sun bayyana cewa harin da aka kai kan dakarun tsaro na soja da na 'yan sanda a yankin Souma da ke arewacin kasar iyaka da Mali sun kai 20.

Yau tsawon shekaru kenan da kasar da yankin yammacin Afirka mai makwaftaka da Mali da Jamhuriyar Nijar ke fuskantar hare-haren 'yan ta'adda wanda kuma suka yi sanadiyar salwantar rayukan mutane da dama.