1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya da Faransa na sa-in-sa tsakaninsu

Mahmud Yaya Azare MAB
October 4, 2021

Bayan janye jakadanta da ta yi daga Faransa, gwamnatin Aljeriya ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga jiragen Faransa bayan kalaman batancin da take ikirarin Shugaba Emmanuel Macron ya yi wa jagororin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/41FJc
Flaggen | Frankreich & Algerien
Hoto: Valery Hache/AFP/Getty Images

Tun a ranar Asabar ne Aljeriya ta janye jakadanta da ke kasar Faransa Mohammed Antar Daoud sakamakon rashin jituwa da ke kara tsananta a tsakaninta da tsohuwar uwar gijiyartata Faransa, da ta taba yi mata mulkin mallaka da shi ne mafi zubar da jini a tarihin mulkin mallaka a nahiyar Afirka. Shugaban Faransa Eammanuel Macron ya yi wata caccaka a jaridar kasarsa mai suna Le Monde da ke kokarin wanke Faransa daga mugun cin zalin da ta yi wa al'ummar Aljeriya a yayin mulkin mallakar da ake cewa, kusan mutane miliyan daya ne yan kasar ta Aljeriya suka mutu,sakamakon fito na fiton da suka yi da Faransa.

A jawabinsa Macron ya nuna mamakinsa kan yadda 'yan Aljeriya suke suffanta mamayar da kasar Turkiyya karkashin mulkin mallakar daular Usmaniya, da kokarin wayar da su da koya musu kyawawan halaye na kwarai, a yayin da suke daukar mulkin mallakar Faransa da cin zali,duk da cewa ba don shi ba, da ba  a san kasar Aljeriya ba, lamarin da ya sanya  kakakin fadar gwamnatin Aljeriya,

Frankreich Air-France Flugzeuge
Jiragen Faransa za su daina kaitsa sararin samaniyar AljeriyaHoto: AFP/B. Guay

Muhammad Lameen Bil ya suffanta shugaban na Faransa da butulu, inda ya sanar da janye jakadan Aljeriya daga Faransa, da hana jiragen Faransa ratsa sararin samaniyar Aljeriya.


Ya ce "Na tabbata shugaba Macron a wannan karon ya yi fatali da irin taka-tsantsan da masu diflomasiyya suke wajen iya bakinsu. Wannan cin mutunci ne ga al'ummar Aljeriya baki daya, kafin ma a yi magana kan jagororin siyasarta, ace shugaban na Faransa zai ce ba don mulkin mallakar Faransa ba, da yanzu ba a san da akwai wata kasa wai ita Aljeriya ba, Wannan jawabin  butulci ne ga kokarin da sabon shugaban Aljeriya ke yi na kokarin dinke barakar da ke tsakanin kasarmu da Faransa."

Masharhanta irin su Abdulazeez Bu Qeerah, kwararren kan alakar Faransa da kasashen Larabawa da ta yi wa mulkin mallaka, ya ce jawabin na Shugaba Macron ba ya rasa nasaba da yakin zaben da yake yi ,ko da kuwa hakan zai kaishi da lashe aman da ya yi a baya.


"Akwai kuri'ar jin ra'ayin jama'a da ke nuna cewa Macron kan iya shan kaye a zaben da ake shirin yi. Ina ganin hakan ya sanya shi canja akala. A da shi da kansa ya sha suffanta mulkin mallakar da Faransa ta yi wa Aljeriya da mummunan laifin yaki da ya zama wajibi a soke shi a tarihi, lamarin da ya yi matukar fusata masu matsanancin ra'ayi a Faransa, wanda a yanzu yake neman dadada musu."

Algerien Macron in Algier 2017
Macron ya rage yawan visa da Faransa ke ba wa 'yan AljeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/A. Belghoul

Dama dai an fuskanci tayar da jijiyoyin wuya tsakanin mahukutan Paris da na Algers bayan da Faransa ta tsaurara matakan ba da takardar visa ga ‘yan kasashen Larabawan yankin Magreb daga ciki har da ita Aljeriyar. Faransa dai na amfani da sararin samaniyar Aljeriya wajen isa ko fita yankin Sahel inda take da dakaru na rundunar Barkhane. Sai dai ta ce hakan ba zai kawo mata wata matsala ba wajen tafiyar da aikinta a yankin ba.