1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alhini ga waɗanda 'yan Nazi suka halaka

February 23, 2012

An yi bikin tunawa da mutanen da ta'asar masu tsattsauran ra'ayin ƙyamar baƙi ta rutsa da su a Jamus.

https://p.dw.com/p/148Ir
Students stand behind a candle altar during a memorial ceremony for victims of far-right violence in Germany at the Concert Hall at the Gendarmen Markt in Berlin, Thursday, Feb. 23, 2012. (Foto:Markus Schreiber/AP/dapd)
Hoto: dapd

A faɗin tarayyar Jamus a wannan Alhamis a daidai ƙarfe 12 na rana aka yi shiru na minti guda don juyayin mutanen da ta'asar masu matsanancin ra'ayin ƙyamar baƙi ta rutsa da su a cikin ƙasar. A birnin Berlin fadar gwamnati shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana irin wannan kisa ta masu ƙyamar baƙin da wani abin kunya ga Jamus. Semiya Simsek na ɗaya daga cikin yaran da suka rasa iyayensu a hannun masu kisan kai dake son sake farfaɗo da ra'ayin 'yan Nazi, ta halarci bikin nuna alhini a birnin Berlin, cewa ta yi.

"A ƙasarmu, a ƙasata dole ne ka iya yin walwala ba tare da la'akari da ƙasarka ta asali ko launin fatarka jikinka, ko adininka ko jinsinka ko kana da naƙasu ba. Ka da ku bari mu rufe idanunmu tamkar mun cimma wannan matsayi da muka sa a gaba."

A nata ɓangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sha alwashin gano waɗanda ke da hannu a kashe kashen domin a hukunta su ta kwatanta wannan lamarin da wani abin kunya ga Jamus.

"Babbar illa ce ga 'yancin walwala da dokokin tsarin mulkin wannan ƙasa, idan aka mayar da mutane a cikin ƙasar saniyar ware ko yi musu barazana ko kuma fatattakarsu. Saboda haka kisan kai da wani gungun masu ƙyamar baƙi suka yi a Thüringen, wani hari ne akan ƙasarmu. Abin kunya ne ga ƙasarmu."

A ƙarshen shekarar bara aka bankaɗo wata aika-aika ta kisan kai da wani gungun 'yan ta'adda da ake wa laƙabi da 'yan Zwickau suka yi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu