1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'amura sun fara kai wa 'yan ƙasar Somaliya iya wuya

December 23, 2011

A shiga wani sabon salo na yaƙin cacar baka tsakanin sojan ƙasar Kenya da mayaƙan Al-Shabab ta yanar gizo

https://p.dw.com/p/13YZd
epa02939023 A Somali government soldier walks in front of a destroyed hotel now serving as an IDP camp (Internally Displaced Persons) in war-torn Somalia's capital Mogadishu, 27 September 2011. Reports states that the African Union Mission for Somalia (AMISOM) is expected to receive 3,000 extra troops from Djibouti and Sierra Leone before December 2011, following the complaints from the forces' commanders claiming that the current number is not sufficient even after the Islamist insurgents of al-Shabab have withdrawn from the city. AMISOM forces are providing protection for the aid agencies that are engaged in humanitarian mission for the famine-hit country. 750,000 people are at imminent risk of death in Somalia while 1.5 million children need immediate assistance including 336,000 children under the age of five who are severely malnourished. EPA/DAI KUROKAWA
Har yau ana cikin mawuyacin hali a SomaliyaHoto: picture-alliance/dpa

A yau dai zamu fara ne da rahoton jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wacce ta bayyana mamakinta a game da yadda ɗan hamayyar ƙasar Kongo Etienne Tshisekedi ya gabatar da kira ga magoya-bayansa da su ta da zaune tsaye bayan da kotun koli ta ƙasar ta tabbatar da nasarar shugaba mai ci Joseph Kabila a zaben Kongon da aka gudanar watan da ya gabata a kuma daidai lokacin da ake bikin rantsar da shugaban domin wa'adi mulki karo na biyu. Jaridar ta ce:

"Tshisekedi dai yayi iƙirarin lashe zaɓen da goyan bayan kashi hamsin da huɗu cikin ɗari na jumullar ƙuri'un da aka kaɗa, amma kuma ba ya da wata shaida game da hakan. Ɗan hamayyar ma dai wuce makaɗi da rawa yayi, inda ya ware ladar kuɗi da zai ba wa duk wanda ya cafke Kabila ya kuma kawo shi gabansa a cikin ankwa. Ta haka Tshisekedi ya ci gaba da take-takensa na yaƙin neman zaɓe, inda yake kira ga 'yan ƙasar Kongo da su shiga ta da zaune tsaye."

DR Congo elections epa03017273 Top opposition leader Etienne Tshisekedi (C) arrives for a news conference at his residence in Kinshasa, the Democratic Republic of Congo, 27 November 2011. The veteran politician vowed to hold a public rally, defying a government order banning political rallies after at least three people had reportedly been killed in a clash on previous day. Presidential and parliamentary elections are scheduled to be held in DR Congo on 28 November 2011 amid concerns over the prospects for fair elections. Tshisekedi, a 78-year-old opposition leader and the head of the Union for Democracy and Social Progress (UDPS), and Vital Kamerhe, a former UDPS member, are among many others who are challenging incumbent Joseph Kabila in the country's second election since the end of a bloody civil war in 2003. Election-related violence has already broken out in parts of the country ahead of the poll. Election official has said on 27 November that there will be no delay and elections will go as planned on 28 November, despite concerns by many that it would be delayed due to the violence and logistical difficulties in the country two-thirds the size of Western Europe. EPA/DAI KUROKAWA
Etienne TshisekediHoto: picture-alliance/dpa

A cikin nata rahoton, a lokacin da ta leƙa Somaliya, jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"A halin yanzun dai al'amura sun kai wa al'umar Somaliya iya wuya. Domin kuwa kusan dukkan ƙasashe maƙobta a yanzu suna wa ƙungiyar Al-Shabab taron dangi ne a ƙasar kuma babu wata alamar cimma zaman lafiya. Su kansu 'yan somaliyan ma dai a ganinsu gwamnatin da aka naɗa ƙarƙashin jagorancin Sharif Sheikh Ahmed tun a shekara ta 2009 ba ta da wani alfanu ga ƙasar."

Kenyan military board a truck headed to Somalia, near Liboi at the border with Somalia in Kenya, Tuesday, Oct. 18, 2011. Kenya said its launch of military operations into southern Somalia against al-Shabab militants was in response to the kidnappings of four Europeans over the last six weeks, though military analysts suspect that Kenya had prepared the invasion before the abductions. (Foto:AP/dapd)
Sojojin Kenya a SomaliyaHoto: dapd

Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta leƙa Somaliyar inda ta gano wani sabon salo na yaƙin cacar baka da aka shiga tsakanin sojojin Kenya da dakarun Al-Shabab ta kan yanar gizo. Ta ce dukkan sassan biyu na ƙalubalanta da cin mutuncin juna ne ta amfani da hanyar sadarwa ta Twitter a yanar gizo.

A daidai lokacin da ake fatan cewar ƙasar Mali zata iya zama abin koyi wajen daidaita al'amuranta domin su dace da canje-canjen yanayin duniya, amma fa ana fuskantar barazanar ɓillar wata mummunar masifa a yankin sahel da ka iya rutsawa da ƙasar, kamar yadda jaridar Neues Deutschland ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:

"Ƙasar Mali na fama da bala'in canje-canjen yanayi, kuma taron duniya akan makomar yanayin da aka gudanar a Durban baya-bayan nan bai tsinana mata kome ba. Taimakon kuɗi na euro miliyan goma da ministan kare muhalli na Jamus Norbert Röttgen yayi wa ƙasar, ba abu ne da ya taka kara ya karya ba dangane da fatan da ake yi na cewar Mali ka iya zama abin koyi a fafutukar daidaita al'amuranta da matsalar canjin yanayin duniyar."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu