1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magajin garin Satambul ya daukar wa 'Yan siyasa alwashi

Zulaiha Abubakar
June 24, 2019

Dubban al'umma sun halarci bikin taya Ekram Imamoglu na jam'iyyar adawa ta CHP murnar lashe zaben magajin gari.

https://p.dw.com/p/3KyIp
Kommunalwahlen in der Türkei | Ekrem Imamoglu
Hoto: Reuters/H. Aldemir

Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan na daga cikin wadanda suka taya Ekram tun a jiya Lahadi jim kadan bayan sabon magajin garin ya godewa al'ummar da suka zabe shi tare da daukar alwashin kawo karshen rarrabuwar kan 'yan Siyasa.

Wannan sauyi dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar, ke yankewa wadanda ke da hannu a yunkurin hambarar da gwamnatin shugaba Erdogan hukunci mai tsauri wadanda suka hada da 'yan siyasar kasar da suka fito daga jam'iyyun adawa.