Jamusawa na zaben sabuwar gwamnati a Lahadin nan
February 23, 2025A safiyar Lahadin nan aka bude rumfunar zabe a nan Jamus, kasa mafi yawan al'umma da karfin tattalin arziki a nahiyar Turai, da ke fama da koma-bayan tattalin arzikin, hadi da matsin lamba kan dokokin shigar bakin haure da kuma makomar Ukraine da alakar Turai da Amurka.
Karin bayani:Jam'iyyun siyasar Jamus na karkare yakin neman zaben Lahadi
Jamus ita ce kasa ta biyu mafi tallafawa Ukraine da makaman yaki don kare kanta daga mamayar Rasha, inda mutane sama da miliyan 59 suka cancanci kada kuri'a, daga cikin mutane miliyan 84 na kasar, wadanda za su zabi 'yan majalisa 630 wato Bundestag.
Zaben na zuwa ne watanni bakwai kafin ainihin lokacinsa, sakamakon rushewar gwamnatin hadaka karkashin jagorancin Olaf Scholz a cikin watan Nuwamban bara, bayan fama da rikicin cikin gida.
Karin bayani:Sabbin manufofin ketare na taka rawa a zaben Jamus
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da masana suka tattara ta nuna cewa 'dan takarar hadakar jam'iyyun CSU/CDU Friedrich Merz ne ke kan gaba wajen samun farin jini a kasar, yayin da jam'iyyar AfD mai ra'ayin rikau da tsananin kyamar baki ke kara samun tagomashi.