1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akalla mutane tara sun mutu a kusa da Mogadishu

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
October 3, 2022

Mutane tara sun gamu da ajalinsu ciki har da wasu kusoshin gwamnatin Somaliya, bayan harin kunar bakin wake da kungiyar Al-shebab ta dauki alhakin kaiwa a Mogadishu.

https://p.dw.com/p/4Hgzi
Somalia, Mogadishu | Anschlag auf Hayat Hotel
Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP/picture alliance

Kwamandan rundunar 'yan sandan kasar Mohamed Moalim Ali ya ce ko baya ga muutane da suka mut, hari ya kuma raunata mutane 10. Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa fashewar motocin biyu da aka kai harin da su ya lalata gidaje da dama. Harin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Somaliya ta ambaci kisan wani jigo na kungiyar Al-Shabab, wanda tun daga farko ta bayar da tukuycin makudan kudi ga duk wanda ya kwarmata mata inda yake.