1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shara ya yi bayyanarsa ta farko a Siriya

August 26, 2012

An yi wa mataimakin shugaban Siriya ganin ƙarshe a ranar 18 ga watan Yuli, lokacin jana'izar wasu jami'an tsaron ƙasar da fashewar Bomb ya kashe.

https://p.dw.com/p/15wxr
epa02982069 Syrian Vice-President Farouk al-Sharaa (R) meets with Wu Sike (L), China's special envoy to the Middle East, in Damascus, Syria, on 27 October 2011. Ahead of the visit, China's Foreign Ministry said the country was sending an envoy to Syria to press ahead with reforms, reiterating that it wants a political solution to the country's ongoing crisis. Earlier this month, China and Russia blocked a UN resolution that aimed at imposing sanctions on Syria. Sike's is on a two-state visit that would also take him to Egypt. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

A wannan lahadin ce, mataimakin shugaban ƙasar Siriya Faruq al-Shara, ya yi bayyanarsa ta farkoa bainar jama'a, sama da wata guda, bayan jite-jiten cewar ya nemi ficewa daga gwamnati. Al-Shara da ake saran zai gana da shugaban komitin kula da harkokin ketare na majalisar dokokin Iran Aladin Borujerdi, an yi masa ganin karshe ne, a wajen jana'izar wasu manyan jami'an tsaron Siriya, da fashewar Bomb ya ritsa da su a ranar 18 ga watan Yuli.

A makon da ya gabata ne dai akayi ta raɗe-raɗin cewar mataimakin shugaban ƙasar ta siriyan, da ke kasancewa babban jami'i, ɗan Sunni daya tilo da ya rage a gwamnatin Bashar al-Assad, yayi kokarin ficewa.

Sakamakon rikicin da Siriyar ta tsinci kanta a ciki dai, gwamnatin Bashar al-Assad ta yi asarar manyan jami'anta, da suka haɗar da tsohon priminista Riad Hijab da fitaccen jami'in soji kuma abokin Assad Janar Manaf Tlass. Mai shekaru 73 da haihuwa dai, mataimakin shugaban ƙasar ta Siriya Faruq al-Shara, ya rike manyan mukamai na tsawon shekaru 30 a gwamnati, a ƙarƙashin shugaba Bashar al-Assad da mahaifinsa Hafez al-Assad.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu