1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabab ta kashe sojoji 17 a Somaliya

Abdul-raheem Hassan
September 29, 2017

Mayakan al-Shabab sun kai hari a sansanin sojoji da ke garin Barire mai tazarar kilomita 50 da Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, inda suka tarwatsa bama-bamai a cikin mota wanda ya yi sanadiyyar ajalin sojoji 17.

https://p.dw.com/p/2kwVF
Anschlag in Gamba (Kenia)
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kamfanin dillacin labarun Reuters ya samu tabbacin harin ne ta bakin kakakin kungiyar al-Shabab din Abdiasis Abu Musab, inda ya ce sun kai harin ne da asubahin Juma'a ya kuma ce sun yi awon gaba da wasu motocin sojojin. Babu dai karin bayani daga bangaren jami'an tsaro da hukumomin gwamnati kan wannan hari da kungiyar ta dau alhaki kawo yanzu.

Amma Ali Nur mataimakin gwamnna a yanki da aka kai harin shi ma ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma bai ba da karin haske kan adadin asarar rayuka da aka samu sanadiyar harin ba.