1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabab ta ce babu 'yunwa a Somaliya

July 22, 2011

ƙungiyar Al-shabab ta ƙaryata matsalar 'yunwa da Majalisar Dinkin Duniya ta ce Somaliya da kuma wasu ƙasashen yankin ƙahon Afirka na fama da ita. Amma kuma ta yarda cewar wasu yankunan Somaliya na fama da ƙanfar ruwa.

https://p.dw.com/p/121nj
Matan Somaliya da ke jiran abinciHoto: dapd

Ƙungiyar Al-Shabab ta Somaiya da ke da tsananin kishin addinin musulunci ta sa ƙafa ta yi fatali da  rahoton da Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta fitar da ke nuna cewar 'yunwa ta afkawa ƙasar. Kakakin ƙungiyar Sheikh Ali Mohammad Rage ya bayyana cikin wata hira da yayi da gidan radiyon Al-Furqaan a yau Jumma'a cewar labarin 'yunwa shafcin gizo ne, kana siyasa ce tsagwaranta. Ko da shi ke dai kakakin na Al shabab ya amince cewar wasu yankunan ƙasar ta Somaliya sun gamu da kanfar ruwa, amma kuma ya ce haramcin da ƙungiyar ta sanya wa wasu ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa na nan daram daƙam.

Wannan sanarwar ta Al-shabab, ta zo ne 'yan makwanni bayan  amincewa da ta yi cewar  asusun  tallafawa ƙananan yara ta MDD wato UNICEF ya kai agajin abinci da magunguna a yankunan da ke ƙarƙashin ikonta. Masu sanya idanu akan abubuwa da ke wakana a ƙasar ta Somalia  na ganin cewar wannan sabon matsayin da ƙungiyar ta ɗauka zai sake taɓarɓara matsalar 'yunwa da ake fama da ita a ƙasashe somaliya, da Habasha da kuma wani ɓangare na kenya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu