1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam ya kashe mutane 10 a Mogadishu

Abdul-raheem Hassan
November 9, 2018

An samu fashewar tagwayen bama-bamai da suka yi sanadiyar rasuwar fararen hula 10 a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya

https://p.dw.com/p/37yDZ
Somalia Explosion in Mogadischu
Hoto: Reuters/F. Omar

Hare-haren sun auku ne a kusa da Sahafi Otal da ke dab da hedikwatar 'yan sanda a babban birnin kasar Mogadishu. Jami'an tsaro a Somaliya sun tabbatar da bindige maharan hudu da suka yi yunkurin shiga ginin Otal din. Shedu sun tabbatar da ganin gawarwakin mutane a kan titi jim kadan bayan harin. Tuni dai kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken. Kasar Somaliya na fuskantar munanan hare-hare daga kungiyar al-Shabaab da ke sanadiyar mutuwar fararen hula da jami'an tsaro.