1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-shaabab ta halaka mutane 11 a Somaliya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 17, 2020

Mayakan kungiyar Al-shaabab a Somaliya sun halaka fararen hula 10 da wani dan sanda daya, a wani mumunan harin da suka kai a Mogadishu a hotel da ake tsugunar da manyan jami'an gwamnati da baki 'yan kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/3h3np
Somalia, Mogadischu I Terrorangriff auf Hotel
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Warsameh

An shafe tsawon sa'o'i hudu ana gumurzu da wasu kwamdojin kungiyar biyar da suka yi garkuwa da jama'a a hotel din, kafin daga bisani sojan kundunbalan kasar Somaliya su kai ga kwace otel a hannun mayakan na jihadi, ko da yake ma'aikatar tsaron kasar ba ta kai ga yin wani karin haske kan yadda aka kubutar da wasu tarin jama'a da aka yi garkuwa da su ba.

Wani kamfanin mai zaman kansa da ke aikin agaji a kasar, ya tabbatar da samun akalla mutun 28 da suka jikkata, a yayin da kuma wasu rahotanni  ke cewa daukacin maharan biyar sun rigamu gidan gaskiya.