1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Al-Burhan ya bukaci MDD ta kawo karshen ayyukanta a Sudan

Mouhamadou Awal Balarabe
November 18, 2023

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya dade da zargin Majalisar ta Dinkin Duniya da haddasa rikici a kasar da yake jagoranta, lamarin da ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin sassa biyu.

https://p.dw.com/p/4Z7qX
Janar Abdel Fattah al-Burhan na fuskantar tsamin dangantaka da MDD
Janar Abdel Fattah al-Burhan na fuskantar tsamin dangantaka da MDDHoto: EL TAYEB SIDDIG/REUTERS

Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kawo karshen aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar da ke fama da yakin basasa. Dama dai Janar Al-Burhan ya dade da zargin Majalisar ta Dinkin Duniya  da haddasa rikici a kasar da yake jagoranta, lamarin da ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin sassa biyu.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke Khartoum ta  aika wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan wata wasika, inda ta nemi UNITAMS mai dauke da fiye da ma'aikata 400 galibin su farar hula, da ta dakatar da aikinta nan take . A halin yanzu dai ana ci gaba da gwabza kazamin fada a Sudan tsakanin sojojin da ke karkashin jagorancin shugaban mulkin sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun sa-kai na mataimakin shugaban kasar Mohammed Hamdan Daglo da aka kora daga bakin aiki.